BAYANI AKAN YANDA MACE ZATA SAKA KAYA (TUFAFI) A CIKIN QUR’ANI





Gabatarwa.
Kafin mu gabatarda dokokin da mace zatabi wurin saka kayanta. Dole ne mu tunatar da wadannan abubuwa masu zuwa:
1-      Al Qur’ani shi kadaine littafin shari’a da Allah ya yarda dashi. (Sura ta 6 Aya ta 114).
2-      Al Qur’ani cikakken littafin ne kuma yayi bayanin komai dalla-dalla daki-daki. (Sura ta 6 Aya ta 38, da Sura ta 6 Aya ta 114, da kuma Sura ta 12 Aya ta 111).
3-        Allah yã kira masu Imani na gaskiya da kada suyarda su fada tarkon bautar wani abu wand aba Allah ba, da guje ma maganganun wasu mutane maimakon bin maganar Allah. (sura ta 9 aya ta 31).
4-      Allah yaa kira wadanda suke haramta abunda Allah bai haramtaba da Makaryata, mushirikai (sura ta 5 aya ta 87, sura ta 6 aya ta 140, sura ta 7 aya ta 32, da kuma sura ta 10 aya ta 59).

Yadda Qur’ani yayi bayanin kayan Mata
Doka ta farko:- Tufafi
يَابَنِيۤ آدَمَ قَدْ أَنزَلْنَا عَلَيْكُمْ لِبَاساً يُوَارِى سَوْءَاتِكُمْ وَرِيشاً وَلِبَاسُ ٱلتَّقْوَىٰ ذٰلِكَ خَيْرٌ ذٰلِكَ مِنْ آيَاتِ ٱللَّهِ لَعَلَّهُمْ يَذَّكَّرُونَ﴿٢٦

Yaa xiyan Adam! Lallai ne mun saukar da wata tufa (kayan sawa) a kanku, tana rufe muku al’aurarku, kuma da qawa. Kuma tufar taqawa wancan ce mafi alheri. Wancan daga ayoyin Allah ne, tsammaninsu suna tunawa.



3-        

Comments

Popular posts from this blog

Will a soul be credited from the deeds of another?

Human rights in Islam

Can the devil bring physical harm or hardship upon the believers?